*SAWTUL HIKMAH ONLINE EDUCATION INC*
*TSARIN ®️EGISTRATION*
1- mutum zai shiga wannan link din domin yin register: https://sawtulhikmah.com.ng/admission
2- Bayan ya bude mutum zai danna "Start New Application" KO "Apply"
3- Idan mutum kan sa zai yi wa register dai ya danna "The Applicant" ma'ana shine me son shiga, idan kuma ɗan sa ko yar sa zai cikewa sai ya danna na biyun, daga nan sai mutum ya cike bayanan sa daidai.
4- ⚠️A tabbatar ana saka Email Address daidai! Rashin saka daidai zai bawa mutum matsala a registration din sa.
5- Bayan mutum ya cike zai kai shi inda zai biya kudin Form Naira Dubu daya ₦1,000, zai ga banking details sai ya dauka ya tura kudin Form din sa, sai ya dauko receipt dinsa evidence ya dora akan inda aka buqata sai yayi submitting.
Ku sani registration ba zai cigaba ba har sai an biya wannan kudin Form din an dora sannan makaranta tayi approving.
6- Bayan anyi approving sai mutum ya cigaba da registration din sa, yayi submitting din form din SA, sai ya jira.
7- Akwai Jarabawar gwaji da za'a bawa mutum yayi akan Aqida tambaya guda 2 kacal! Yana kammalawa sai yayi submitting ya tura. Zai jira saqon Admission daga ofishin sakataren makaranta ta email din sa.
8- Za'a yi approving tare da bawa mutum Ajin sa na karatu da lambar registration din sa. Da kayan karatu da timetable da pdf na litattafan sa. Kuma zai ga WhatsApp link ta email din sa da zai shiga don ganin saqonni da nuna masa yadda ake amfani da App din makaranta.
9- Akwai Kudin Term da dalubi zai biya, ₦2,000. Duk Term din karatu #2000. A shekara ₦6,000.
10- Bangaren enterprenuership ana yinsa ga dukkan halqat a babin subjects, ana yin sa daban kuma a matsayin Diploma in Shaa Allah.
Jazakumullahu bil jannah.