FALALAR YIWA ANNABI SALATI

FALALAR YIWA ANNABI SALATI


FALALAR YIWA ANNABI SALATI

Falalar Salati ga Annabi

Allah Madaukaki Ya ce: {Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga Annabi. Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da yi masa sallama domin amintarwa gare shi.}



Manzon Allah ﷺ yace:
Ka yawaita yi min salati a daren Juma'a da ranar Juma'a. Duk wanda yayi min salati sau daya, Allah zai yi masa salati sau goma.
Sahihul Jami'i 1209
Manzon Allah ﷺ ya ce:
Mutanen da suka fi kusanci da ni ranar kiyama su ne wadanda suka fi yawaita salati gare ni.
Sahih al-Targheeb 1668
Manzon Allah ﷺ ya ce:
Allah yana da mala'iku masu yawo a doron kasa, suna isar mani gaisuwar al'umma ta (Salati).
Sahihul Nasa'i 1281
Manzon Allah ﷺ ya ce:
Ku yawaita salati gareni, domin Allah ya sanya Mala'ika a kabarina. Idan wani mutum daga cikin al'ummata ya yi mini salati, sai wannan mala'ikan ya ce da ni: Ya Muhammadu, dan wane-da-wane, ya aiko da sallamarsa zuwa gare ka.
Sahihul Jami'i 1207
Manzon Allah ﷺ ya ce:
Ba mai yi min salati face sai Allah ya dawo min da raina har sai na mayar masa da gaisuwa.
Sahih Abi Dawud 2041
Manzon Allah ﷺ ya ce:
Ku yi mini salati, ku gaishe ni, domin salatin ku tana isa gare ni a duk inda kuke.
Sahih al-Jami' 3785
Manzon Allah ﷺ ya ce:
Wanda ya yi min salati, Allah zai yi masa salati goma.
Sahih Muslim 384
Ya Allah kayi salati da sallama ga Annabinmu Muhammad ﷺ


Abou Khadeejatu Assalafeey
01/02/1446
25/07/2025


  • Share

COMMENTS