Hadisin Ibn Adi wanda ya ruwaito daga Ibn Abbas, cewa, Manzon Allah ya ce: “Duk wanda ya haddace hadisai arba’in daga Sunnah ga al’ummata, to ni zan kasance mai ceto a gare shi, kuma shaida ranar kiyama”.
kamar yadda yan uwa daluban ilimi suka sani, mun kammala haddar hadisai 100 a karo na biyu, to in shaa Allahu zamu ƙaddamar da cigaban haddar Hadisan Sahihaini guda 100 wanda suka shafi babuka masu fadi da muhimmanci musulmi ya san su a karo na 3, muna kira da duk mai kishi da haqaza to ya daure da karanta Maganganun Annabi da fahimtar su musamman a wannan lokaci da ake yaqar su....
Tsarin:
Karatun Kyauta ne!
Zaa gabatar da karatun ta hanyar online ne, akwai whatsapp group da aka bude don turo da saqonni da karatuttukan.
Duk wanda zai shiga ya tabbatar yana da Google Meet, ko Manhajar ZOOM, domin tanan zaa dinga karbar hadda da sauraro.
Har Yara Ƙanana zaa iya sakawa, don su yi, saboda haka mutum zai iya yiwa kan sa Register da 'ya'yansa ko matan sa.
Wajibi ne kiyaye lokacin bada karatu da zuwa akan lokaci, sannan bazamu yarda da fashi babu dalili ba, duk wanda ya jera sati 2 bai bada hadda ba, zamu cire shi!
Karatun Baƙi ne hade da fassara kawai, kuma duk sati xaa bada haddar hadisai 5 ne.
Karatun ya kunshi maza da mata ne.
Akwai Certificate ga wadanda sukayi Nasarar kammalawa.
Lokacin bada karatu da yin sa, karfe 9:00PM (Lahadi, Litinin).
Ga duk mai sha'awar shiga, sai ya danna link din da kasa domin cikewa