*????DAURAR LITTAFIN AQEEDATUL ƊAHAWIYYA ????* *????DAURA TA 5️⃣* Assalamu Alaikum Warahmatulah wabarkatuh, muna sanar da yan uwan mu daluban ilimi, musamman wanda suke tare da mu a karatuttukan mu da muke gudanarwa da sauransu, cewa in shaa Allahu zamu saka daura ta 5 cikin babin aqida da muke gabatarwa na littafin AQEEDATUL ƊAHAWIYYA. Mun saka littafin ne bayan kammala littafin Manzumatul Ha'iyya na Imam Abi Dawud, duba da shima wannan jerin ne na aqida/Tauhidi. *Tsarin:* 1- Karatun Kyauta ne! Amma za'a yi register na cike form da ke ƙasa. 2- Za'a gabatar da karatun ta hanyar online ne, akwai whatsapp group da aka bude don turo da saqonni da karatuttukan. 3- Karatun zai gudana ne ta hanyar recorded audio, kuma munyi kokarin tsara karatun bisa doro na karantawa da bayani daidai gwargwado, ma'ana babu tsawwalawa a sharhi. 4- Zamu so a haddace baitukan, sakamakon tsarin karatun Abyat hadda ake musu. Amma ba dole ba ne, an so ne. 5- Idan wa'adin lokacin saurare ya cika mutun bai saurara ba, zamu cire shi kai tsaye. 6- Yadda zaa gane dalubi ya saurara shine, zaiyi alama reaction akan audio da aka turo 7- Karatun ya kunshi maza da mata ne. 8- Akwai Certificate ga wadanda sukayi Nasarar kammalawa da jarabawar gwaji a karshe. 9- Zamu rufe da wuri yadda aka saba, ranar Talata da safe 24/06/2025, saboda haka a harzanta cikewa da wuri. 10- Ga duk mai sha'awar shiga, sai ya danna link din da ke ƙasa don yayi register:???? https://surveyheart.com/form/6856d5631d2e9337fc7936aa *⚠️Deadline: 24/06/2025 da dare* 08032312988 _Wannan Program din, zauren Sawtul hikmah ne suka dauki nauyin kawo shi, Allah yasaka musu da alheri_ *????️ZAUREN SAWTUL HIKMAH MEDIA TV* 08032312988 [email protected]