Mafi kwayun ranakun duniya

Mafi kwayun ranakun duniya


Mafi kwayun ranakun duniya

Mafi kyawun ranakun duniya 🕋

🌱 In shaa Allahu mafi alkhairin ranakun duniya zasu kasance tare da mu.
(kwanaki Goma ga Zul-Hijjah)


📌 Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: "Babu wasu kwanaki da ayyuka na qwarai suka fi soyuwa a wurin Allah fiye da wadannan kwanaki goma". Abu Dawud ya ruwaito

✔️ Daga cikin ayyukan qwarai da aka shar'anta a cikin wadannan ranaku masu albarka akwai:

▪️ Ambaton Allah Ta'ala
Mafi girman zikiri shine karatun Alqur'ani. Allah Ta’ala ya ce: {Wadanda suka yi imani, kuma zukatansu suka natsu da ambaton Allah. To, da ambaton Allah zukata suka tabbata.} [Ra'd: 28].


▪️ Kabbara
Mafifitan nau'o'in takbir su ne:
(الله أكبر الله أكبر لا إله إلا الله، والله أكبر الله أكبر ولله الحمد).
(Allah mai girma da daukaka, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah mai girma da daukaka, kuma godiya ta tabbata ga Allah).


▪️ Yawaita Sallah
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Ka yawaita yin sujada ga Allah, domin ba za ka yi sujada ga Allah sau daya ba, face sai Allah ya daukaka maka darajoji, kuma ya kankare maka zunubi”. Muslim ne ya ruwaito shi.


▪️ Azumi
Musamman azumin ranar Arafah; Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: *“Azumtar ranar Arafah ina fatan Allah ya kankare zunuban shekarar da ta gabace ta da na shekarar da ke bayanta."* Muslim ne ya ruwaito shi.


▪️ Sadaka
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: *“Sadaka tana kashe zunubi kamar yadda ruwa ke kashe wuta”.* Tirmizi ne ya ruwaito shi.


▪️ Hadaya/Layya
Layya tana daga cikin ladubban da Allah madaukaki ya ce: *" Kuma duk wanda ya girmama ibadojin Allah, to lallai yana daga ayyukan taqawan zukata* " [Hajji: 32].


♻️ _Allah ya sakawa duk wanda ya yaɗa wannan saqon zuwa ga wani, ya maye gurbin bakin ciki da damuwa da farin ciki da jin dadi gare shi_ ..
🕋 ▪️❀﷽❀ ▪️🕋

✍️Abou Khadeejatu Assalafeey 🌱🌻 🌹🌾
29/11/1446.
27/05/2025.

Danna shudin rubutun ƙasa don karantawa duka.

Kwanaki mafi kyawu a duniya


  • Share

COMMENTS