*TARIHI DA KAFUWAR SHAFIN 🎙️ZAUREN SAWTUL HIKMAH MEDIA TV🎙️*
Bayan dukkan cikakken yabo tare da godiya ga Allah Madaukaki Bisa dukkan Ni'imominSa, Muna sake jaddada Godiya gare shi bisa Ni'ima ta musulunci da fahimtar Sunnah. Alhamdulillah. Bayan haka:
Masu karatu, Assalamu Alaikum Warahmatulah wabarkatuh, Wannan Kafa Mai Albarka ta Sawtul hikmah Media Tv, zata bada taqaitaccen tarihin ta, gwagwarmaya, nasarorin ta, kalubale dss, a wannan shafin in shaa Allah.
Da farko, wannan Kafa an bude ta ne a shekarar 2016, karkashin jagorancin mutum 3-5, kuma babbar manufar bude ta shine yunkurin yada Addinin musulunci ta kafafen sadarwa da Waazantarwa tare da Fadakarwa. Wanda Shafin ya kai shekaru 8 da kafuwa a kafafen sadarwa yanzu.
Asalin kafuwar Sawtul hikmah shine, haɗaka ce ta yan uwa daluban ilimi masu son sunnah da yaɗa ta, wanda kafin Sawtul hikmah, muna da zaure mai suna KITABU WAS SUNNAH, aciki ake gudanar da dukka harkokin da'awa tare da taimakon manyan malaman mu da yan uwa manyan dalubai, wanda daga baya wasu yan uwa Ma'abota alheri suka nemi Hadewar mu da su don mayar da zauren zuwa MIFTAHUS SUNNAH (wato mabudin Sunnah) 😊, kuma Alhamdulilah bayan Hadewa, tafiya ta kuma girmama tare da kafuwa, wanda daga baya bayan faruwar wasu matsaloli da aka fuskanta a tafiyar, ya jawo ainihin shi KITABU WAS SUNNAH Ya ware kan sa daga ciki, sai kuma aka mayar dashi zuwa SAWTUL HIKMAH DAAWAR SUNNAH A SOCIAL MEDIA'S!
Dalilin wannan rabuwa yana da faɗin sosai, kuma babban dalilin baya huce sauka daga kan ainihin manhajin da aka faro akai da wasu yan uwa sukayi da sauran su. Wanda shine ya janyo hakan, amma Alhamdulillahi bayan tabbatar da sunan Sawtul hikmah a shekarar 2016, wanda wanda suka yi musharaka ciki sun haɗ da:
*Abdallah Auwal Abdallah (Abou Khadeejatu Assalafeey)
*Abdulmalik Umar Sani R/lemo.
*Ibrahim Khalil.
*Malama Salamatu Idris (Ummu Muhammad).
*Malama Maryam Misrah (Ummu hamdam wa hamid).
Wannan sune bayin Allahn da suka kafa Sawtul hikmah da tafiyar ta a wannan lokacin, sai sauran yan uwa da sukayi joining daga baya wajen taimakawa cikin tafiyar, Allah yasaka musu da Aljanna. Amin
MANUFAR KAFA SAWTUL HIKMAH DA DALILIN KASANCEWAR TA ONLINE:
Babbar manufar kafa Sawtul hikmah itace yunkurin yada Addinin musulunci, bisa Qur'ani ta hanyar sunnar Manzon Allah (S.A.W), da fahimtar magabata na kwarai. Da karantawa a bisa manhajin Ahlul Sunnah Wal Jama'a ta fannoni daban daban. Tare da karantar da mutane Aqida ta kwarai da rushe bidi'a da shirka da addinin shi'a a duniyar Hausawa ta media.