Career

Ina wannan rubutun ne tare da gagarumin alfahari da godiya ga ALLAH a matsayina na shugaban wannan babban zaure mai albarka. Sunana Abdallah Auwal Abou Khadeejatu Assalafeey, kuma ina jin daɗin ganin cewa wannan zaure ya kai har zuwa wannan babban matakin!

Cibiyarmu ta zauren Sawtul hikmah ba wurin karatu ba ce kawai; amma sai dai al'umma ce mai fa'ida, inda ta ke bunƙasa karantarwa da raya ruhin al'umma bisa imani, tare da cika musu mafarkan su. Sawtul hikmah duk da kasancewar ta kafa a iya dandalin whatsapp, amma Alhamdulillah ta cimma manyan nasarorin masu girma wanda sinadarin shine tsantsar dagewa da kuma yi domin ALLAH.

Yayin da muke shiga sabuwar shekara ta ILIMI, wacce muke cika shekara 9 cif da kafuwar, ina cike da murna da alfahari na ganin wannan nasarorin da muke samu.

Duk wannan matakin da muka kai Admins da malamai wanda suka sadaukar da kai suka himmatu don haɓaka wannan ƙafa bazaa manta da su ba, domin ba don jajircewar su da kokarin su ba, da bamu kawo zuwa inda muke a yau ba. Alhamdulillahi cikin ƙwarewar su har cikin ɗalibi muka samu masu ƙoƙari don samar da yanayin da ke haɓaka ƙirƙira, sana'a, kasuwanci, karatu dss abubuwa masu mahimmanci.

In shaa Allahu Tare, za mu ƙarfafa ɗalibanmu masu shigowa da na ciki, don fuskantar dukkan ƙalubale tare da juriya da tunkarar kowace dama da zamu samu.

Haɗin kai tsakanin da kyakkyawar mu'alama da ɗalibai, iyaye, da manyan malamanmu shine tushen falsafar ilimin mu da nasarar mu. Mun yi imani da cewa ƙarfin haɗin kai, da kuma yin aiki tare, za mu iya haifar da yanayi wanda ke ƙarfafa yan uwa taka a musulunci da daukaka addini.

Yayin da muke tafiya cikin shekarun karatu baya, ina tunatar da mu mahimmancin mutunta juna, buɗewar sadarwa, da sadaukarwa tare don taimakon juna. Ina ƙarfafa kowane ɗalibi da ya rungumi tafiyar neman ilimi, yin tambayoyi, da bin malamai na kwarai, Makarantarmu tana nan don yi wa kowa jagora, bada goyan baya, da ƙarfafawa.

Iyaye, da membobin mu na dukkan social Media's haɗin gwiwar ku yana da kima sosai wurin mu. Shiga cikin ilimin yaranku shine ginshiƙin nasarar su. Tare, bari mu samar da yanayi inda ɗalibanmu za su bunƙasa ilimi, zamantakewa, da kuma sana'ana.

A ƙarshe, ina farin ciki game da ban mamaki na ilimi da nasarorin da ke jiran kowane memba da dalubi na makarantarmu. Mu fara wannan tafiya tare, tare da ƙwazo, sadaukarwa, da hangen nesa don samun nagarta da ilimi mai albarka.

Nagode da bamu amanar Tarbiyyar ku da ilimin ku. Allah ya hada Fuskokin mu gidan Aljanna. Amin

Check for Vacancies